Kungiyar likitocin Najeriya reshen jihar Filato a ranar Laraba ta ce ta kama wani likitan bogi bisa zarginsa da gudanar da aikin jinya a makarantu da wuraren ibada a jihar.
Shugaban NMA na jihar, Dokta Bapigaan Audu, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a wata sanarwa da ya sanya wa hannu tare da jami’in hulda da jama’a na kungiyar, Dokta Istifanus Bako.
A cewar NMA, wanda ake zargin ya yi amfani da sunaye daban-daban wajen gudanar da wannan aika-aika.
An kama shi ne a babban birnin Jos bayan wani bincike da kungiyar ta kaddamar tare da jami’an ma’aikatar lafiya ta jihar.
An tattaro cewa daga bisani an garzaya da wanda ake zargin zuwa hedikwatar ‘yan sanda da ke Jos inda aka tsare shi.