Tantita Private Security Services Limited (TSSL) kamfanin samar da tsaro mai zaman kansa da gwamnatin tarayya ta bawa aikin yaƙi da satar ɗanyen man fetur a yankin Niger Delta ya kama wani jirgin ruwa ɗauke da man sata har lita dubu 80000 a jihar Bayelsa.
Warredi Enisuoh daraktan ayyukan yau da kullum na kamfanin ya ce an kama jirgin ne da tsakar daren ranar Lahadi a jihar Bayelsa aka kuma tasa keyarsa ya zuwa Oporozza dake jihar Delta.
Enusuoh ya ce jirgin mai suna MT Harbor Spirit an kama shi ne lokacin da yake ɗaukar mai daga rijiyar mai ta Segana dake gaɓar ruwan Bayelsa.
Ya ce an kama jirgin ruwan da haɗin gwiwar jami’an tsaron soja da na kamfanin na TSSL bayan da suka jima suna bibiyar ayyukan jirgin.
Enusuoh ya ƙara da cewa yan Najeriya 12 ne a cikin jirgin lokacin da aka tsare jirgin.