An kama ƴan kungiyar IPOB 18 da ake zargi da kisan ƴan sanda

Rundunar yan sandan jihar Imo ta kama mutane 18 da ake zargi da zama yan kungiyar IPOB da suke da hannu a kisan ƴan sanda biyu a mahadar Ahiara dake karamar hukumar Ahiazu-Mbaise ta jihar.

Jami’an tsaron da suka tsaya shan mai a gidan man BOEK Petroleum a ranar Litinin sun fuskanci farmaki daga wasu ƴan bindiga da ake zargin ƴan IPOB ne.

Maharan na sanye ne da kayan sojoji inda suka farma ƴan sandan babu zato dake motoci uku kuma suka riƙa harbin kan me uwa da wabi.

A cewar Henry Okoye mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ya ce yan sandan biyu da aka kashe a harin sun haɗa da DPO na Ahiazu-Mbaise da kuma wani insifecta.

Ya ce mutanen na cigaba da amsa tambayoyi a yayin da ake cigaba da bincike.

More News

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye aikinsa na wani lokaci

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya ajiye aikinsa na wani lokaci domin tunkarar matsalar lafiya.Mista Ngelale...

Ali Jita ya koma jam’iyar APC daga NNPP

Mataimakin shugaban majalisar dattawa dattawa, Sanata Barau Jibrin ya karɓi fitaccen mawakin Kannywood, Aliyu Isa Jita daga jam'iyar NNPP ya zuwa jam'iyar APC. Ali Jita...

An yi jana’izar mutumin da ya ƙirƙiri tutar Najeriya

Iyalan marigayi, Pa Taiwo Akinkumi mutumin da ya ƙirƙiro tutar Najeriya sun yi bikin binne shi bayan da gwamnatin tarayya ta gaza cika alƙawarin...

‘Za a ƙara wa ƴan bautar ƙasa na NYSC alawus’

Babban daraktan hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC) Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa ‘yan bautar kasar cewa za a kara...