An kai wa gwamnan Kogi hari

Gwamnatin jihar Kogi ta ce jami’an tsaro sun dakile wani yunkurin kashe gwamnan jihar Yahaya Bello a kan hanyarsa ta zuwa wani aiki daga Lokoja zuwa Abuja.


Sanarwar da kwamishinan yada labarai da sadarwa na jihar, Kingsley Fanwo ya fitar a Abuja, ya ce an kai harin ne da misalin karfe 4 na yamma a ranar Lahadi.


Ya ce: “Maharan da ke sanye da kakin soji sun tare ayarin motocin Gwamnan suka yi ta harbe-harbe kan motarsa da sauran motocin da ke cikin ayarin. Sai da jami’an tsaro da ke tare da Gwamnan suka shiga cikin gaggawa domin dakile shirin shedan na sojojin da ba a san ko su waye ba.

More News

Tayoyin jirgin saman Max Air sun fashe a Yola

Jirgin saman kamfanin Max Air ƙirar Boeing 737 mai rijistar namba 5N-ADB dake ɗauke da fasinjoji 118 da ma'aikata 6 ya gamu da matsala...

Tinubu ya amince da mafi karancin albashi na N70,000

Shugaba Bola Tinubu ya amince da N70,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikatan Najeriya, inda ya yi alkawarin sake duba dokar mafi karancin...

ÆŠan majalisar wakilai ta tarayya ya mutu

Hon. Olaide Akinremi Jagaba mamba a majalisar wakilai ta Najeriya dake wakiltar mazaɓar Ibadan North a majalisar ya mutu. Kawo yanzu babu cikakken bayani kan...

Mutanen Isra’ila sama da rabin miliyan sun tsere saboda yakin Gaza

Mutanen Isra'ila sama da rabin miliyan ɗaya ne suka fice daga ƙasar kuma ba su koma ba a watanni shida na farkon yaƙin Isra'ila...