An kai harin kunar bakin wake a wurin daurin aure a Borno

A safiyar ranar Asabar ne wani dan kunar bakin wake ya kai hari a wani daurin aure a garin Gwoza na jihar Borno, inda ake fargabar mutuwar mutane da dama.

Wadanda abin ya shafa sun hada da baƙi, a cewar rahotanni da dama.

Wannan al’amari dai ya sa mutane sun fara tuna yadda ake yawan kai hare-haren kunar bakin wake a Borno a lokacin rikicin Boko Haram.

Ana ci gaba da samun cikakken bayani kan harin, kuma kawo yanzu ba a tabbatar da adadin wadanda suka mutu ba.

More from this stream

Recomended