
A jikkata wasu jami’an tsaro a wani hari da yan bindiga su ka kai kan jerin ayarin motocin gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ranar Asabar akan hanyar Abuja zuwa Lokoja.
Kingsley Fanwo, kwamishinan yaɗa labarai na jihar ya ce an kai harin ne a kusa da sansanin sojojin ruwa dake da tazarar ƴan kilomitoci daga Lokoja babban birnin jihar.
Kwamishinan ya ce lamarin da ya faru da misalin karfe 12:30 na rana ya jikkata mutane da dama ciki har da jami’an tsaro.
“Mun godewa Allah gwamnan mu ya bar wurin ba tare da ko kwarzane ba kuma babu dalilin shiga cikin firgici.” A cewar Fanwo.