
Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Kisan Janar Soleimani ka iya kara rura wutar rikici a yankin
An harba rokoki da dama kan sansanonin Jadriya da Balad na dauke da dakarun kasar Amurka da na Iraki a Baghadaza ranar Asabar, kamar yadda rundunar sojan Iraki ta bayyana.
Sansanonin Jadriya da Balad ana ayyana su ne a matsayin yankin mai aminci da ma’aikatan difilomasiyya ke gudanar ayyukansu.
Sai dai kamfanin dillancin labarai na Reauters ya ruwaito cewa ba a samu rasa rai ba ko jikkata.
“An harba rokoki da yawa kan dandalin Celebration Square da Jadriya a Baghadaza da kuma sansanin sojan sama na Balad amma ba a rasa rai ba ko jikkata,” a cewar wata sanarwa daga rundunar sojan Iraki.
- Ba mu kashe Janar Soleimani don haddasa yaki ba -Trump
- Wane ne Qasem Soleimani – babban kwamandan Iran da Amurka ta kashe
Babu tabbaci game da kungiyar da ta kai harin, amma mayaka masu biyayya ga kasar Iran a yankin ka iya yunkurin daukar fansar kisan Janar Qasem Soleimani, kwamandan rundunar sojin Iran, wanda Amurka ta hallaka ranar Alhamis a Baghadaza.
Harin na birnin Baghadaza ya tayar da kura tare da fargabar yiwuwar barkewar wani sabon rikici a yankin Gulf.
A yau Asabar dubun dubatar masu tattaki a Iraqi sun la’anci Amurka yayin makokin janar din, wanda za a mayar da gawarsa zuwa Iran, inda za a binne shi a kauyensu.
Amurka ta ce ta kashe Janar Soleimani domin kauce wa yaki. Gwamnatin Shugaba Trump ta bayyana marigayin a matsayin wanda ya kitsa hare-haren da Iran ke kaiwa.