Akalla mutane biyar ne suka mutu sannan wasu 11 suka jikkata bayan wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun harba makamin roka a wani gari a jihar Borno.
Wasu kwamandojin mayakan jihadi biyu sun shaida wa kamfanin dilancin labaren AFP a ranar Lahadi cewa mayakan da dama sun yi yunkurin kutsawa garin Damboa da yammacin Juma’a amma sun fuskanci turjiya daga jami’an tsaron da ke aiki tare da sojojin.
Harin dai shi ne na baya bayan nan a rikicin jihadi a Najeriya na tsawon shekaru 14 a yankin arewa maso gabas, inda mutane 40,000 suka mutu yayin da sama da miliyan biyu suka rasa muhallansu sakamakon yakin tun shekara ta 2009.