![](https://arewa.ng/storage/2020/04/An-gano-mai-cutar-Korona-da-ya-tsere-a-jihar-Borno-–-AREWA-News.jpg)
An gano daya daga cikin masu cutar Korona da suka tsere a jihar Borno. Kwamishinan lafiya na jihar, Salisu Kwayabura shi ne ya tabbatar da haka.
Kwayabura ya bayyana haka ne cikin wani sako da ya wallafa ranar Litinin a shafin Facebook na gwamnatin jihar.
Ya ce an gano Abbas Kaka Hassan mai shekaru 24 da misalin karfe biyu na dare a Maiduguri.
Hukumomi a jihar sun bayyana bacewar Hassan tare da wata mata da aka yi musu gwaji tare a asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri bayan da ya kashe wayarsa da kuma ta mahaifiyarsa.
Kwamishinan ya ce an gano marar lafiyar ne a gidansu inda aka same shi cikin mawuyacin hali kuma tuni aka dauke shi ya zuwa cibiyar da ake killace masu cutar Korona a jihar inda yake numfashi da taimakon na’ura.