An tabbatar da ganin jinjirin watan Ramadan 1445/2024 a kasar Saudiyya.
Kamar yadda labarin ke yaduwa, ana ci gaba da shirye-shiryen fara Sallar tarawihi a Masallatan Harami guda biyu bayan Sallar Isha’i.
Wannan wata dai ana sa ran zai hada kan Musulmin duniya baki daya wajen gudanar da azumi da addu’o’i.