An fi fuskantar yanayin zafi daga shekarar 2010 zuwa 2019 | BBC Hausa

heat

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

An tabbatar cewa shekarar 2010 zuwa karshen 2019 su ne shekarun da aka fi fuskantar yanayin zafi kamar yadda wasu hukumomi uku na duniya suka bayyana.

A cewar Nasa da Noaa da kuma ofishin hukumar kula da yanayi a Birtaniya, shekarar da ta gabata ita ce shekara ta biyu da aka fi yin zafi idan aka yi duba zuwa 1850.

Shekaru biyar din da suka gabata su ne aka fi yin matsanancin zafi cikin jerin shekaru 170.

Ofishin kula da yanayin ya ce da alama shekarar 2020 na iya fuskantar irin wannan yanayin.

Shekarar 2016 ce shekarar da ta fi fuskantar zafi a tarihin inda yanayin ya karu sakamakon sauyin yanayi na El Nino.

Bayanan da aka samu ba su zo da mamaki ba saboda hukumar kula da yanayi ta duniya ta ce da alama yanayin zafi ya zo karshe a farkon Disambar shekarar da ta gabata.

Ofishin kula da yanayin wanda yake samar da bayanan yanayin HadCRUT4, ya ce shekarar 2019 ta kasance kan ma’aunin yanayi 1.05 sama da matsakaicin lokaci daga 1850-1900.

A shekarar da ta gabata, an yi zafi sosai a yankin Turai cikin watan Yuni da Yuli inda yanayin ya kai maki 46 a Faransa ranar 28 ga watan Yuni.

An kuma samu irin wannan yanayin a Jamus da Netherlands da Belgium da Luxembourg da kuma Birtaniya kan maki 38.7.

Australia kuma ta fuskanci yanayin zafi a lokacin bazara.

Magance sinadarin carbon na janyo kalubale

Daga Roger Harrabin( Mai sharhi kan muhalli)

Yayin da yanayin ke ci gaba da karuwa, kokarin da ake na rage iska mai zafi na ci gaba da fuskantar koma baya dai-dai lokacin da kimiyya ke cin karo da siyasa.

Birtaniya misali, ta fafata kafin ta samu damar karbar bakuncin taron shekara-shekara kan sauyin yanayi na majalisar dinkin duniya a karshen shekara inda ake kira ga kasashe da su rage yawan gubar da suke fitarwa ta iska.

Kuma Boris Johnson ya ce yana son Birtaniya ta jagoranci kasashen duniya kan sauyin yanayi.

Sai dai a farkon mulkinsa ne aka fara zarginsa da yin watsi da wasu tsare-tsarensa.

Ya sha alwashin rage harajin Fam 13 kan jirage a Birtaniya saboda ayyukan yi na cikin hadari.

Hakan ya ci karo da shawarar da kwamitin kula da sauyin yanayi ya ba sa a hukumance kan cewa akwai bukatar mutane su rage yawan tafiye-tafiye don kudin tafiye-tafiyen ya karu a maimakon ya ragu.

Wannan zai dagula lissafi cikin shekaru masu zuwa yayin da sauyin yanayi ke ci gaba da haifar da matsaloli ga siyasa.

Yayin da hukumomin da suka gudanar da binciken suke da bambanci kan kididdigar da suka fitar, hukumar kula da yanayin ta duniya ta gudanar da wani bincike inda ta yi amfani da wasu bayanai daga cibiyar sauyin yanayi ta Copernicus da hukumar kula da yanayi ta Japan.

Hakkin mallakar hoto
NASA

“Alkaluman da suka tattara sun nuna cewa shekarar 2019 ta bi sahun jerin shekarun da suka fuskanci zafi daga 2015,” a cewar Dr Colin Morice daga ofishin kula da yanayi na cibiyar Hadley.

“Kowace shekara 10 daga shekarun 1980 sun kasance cikin zafi idan aka kwatanta da sauran shekarun da suka gabata.”

Masu bincike sun ce fitar da sinadarin carbon sakamakon ayyukan bil adama shi ne babban dalilin daidaita karuwar yanayin a shekarun baya-bayannan.

More News

Bayan fitowa daga gidan yarin Joshua Dariye na shirin tsayawa takarar sanata

Matukar ba a samu sauyi daga baya ba to kuwa tsohon gwamnan jihar Filato, Joshua Dariye zai ayyana aniyarsa ta tsayawa takarar majalisar dattawa...

Duk wanda ya ce Najeriya kalau ta ke to a binciki kansa-Obasanjo

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya ce har yanzu Najeriya ba ta kai matakin da yakamata ace ta kai ba a yanzu. A cewar...

Yan bindiga sun sako karin mutane 7 daga cikin fasinjojin jirgin kasar Abuja zuwa Kaduna

Yan bindiga da suka yi garkuwa da fasinjojin jirgin kasar da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna sun kara sako mutanen 7 daga cikin...

Farashin ɗanyen man fetur ya yi kasa a kasuwar duniya

Farashin gangar danyen mai ya fado kasa da dala $95 a ranar Talata. Faduwar tasa na zuwa ne biyo bayan saka ran da ake na...