An fargabar gini a rufta da dalibai da dama a Jos

Wani gini mai hawa biyu na makarantar Saint Academy da ke Jos ya ruguje, inda dalibai da dama ake fargabar abin ya rutsa da su.

Ginin da ya kunshi ajujuwa da ofisoshi ya ruguje ne a ranar Juma’a, yayin da daliban ke rubuta jarabawar zango na uku.

Wakilin Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), wanda ke wajen da lamarin ya afku, ya ruwaito cewa ƙasan benen na dauke da daliban makarantar sakandire ta daya (JSS1), yayin da manyan daliban ke a saman benayen.

NAN ta ruwaito cewa, a lokacin da ake gabatar da wannan rahoto, hukumar agajin gaggawa ta jihar Filato (SEMA) na ci gaba da aikin ceto.

Mista Sunday Abdu, Sakataren zartarwa na Plateau SEMA, ya shaida wa NAN cewa hukumar ta tattara jami’anta da hukumomin da abin ya shafa zuwa wurin da lamarin ya faru domin ceton gaggawa.

Abdu ya ce a halin yanzu jami’an hukumar ci gaban birnin Jos (JMDB) da sauran su suna wurin da kayan aikin motsa kasa domin kwashe baraguzan, da kuma kokarin ceto yaran.

More from this stream

Recomended