Hukumar FCTA dake kula da birnin tarayya Abuja ta fara rushe gine-gine sama da 500 da aka yi ba bisa ka’ida ba a kasuwar Karmo dake Abuja.
Mukhtar Galadima daraktan sashen dake kare birnin daga bunƙasa ba tare da tsari ba ya ce an fara rushe-rushen ne biyo bayan ƙarewar wa’adin awanni 24 da aka bawa ƴan kasuwar na su tashi daga wurin.
Galadima wanda ya samu wakilcin Garba Jibril mataimakin darakta dake lura da yankin Karmo da sauran wasu yankuna ya ce an sanar da dukkan mutanen da abun ya shafa inda ya ƙara da cewa anbi dukkanin wata ka’ida kafin a fara aikin.
“A fili yake ƙarara mutane suna shafe a wanni kafin su wuce ta titin musamman ranar da kasuwa take ci,” ya ce.
“Domin shawo kan wannan matsalar ministan Abuja Nyesom Wike ya bayar da umarnin rushe gine-gine da aka yi ba bisa ka’ida ba,” ya ce.
Galadima ya yi kira ga ƴan kasuwar da abun ya shafa da su koma kasuwannin da aka samar .