Al Arabiya ta ce rundunar sojin saman kasar ta tarwatsa makaman masu linzamin.
Gwamnatin Yemen wadda Saudiyya ke mara wa baya ta yi Allah-wadai da harin, inda ta bayyana cewa kai hari birnin mai tsarki “mummunan aikin ta’addanci ne.”
A makon jiya ne ‘yan tawayen Houthi suka fara shirye-shiryen janyewa daga tashar jirgin ruwa ta Hudaydah da wasu kananan tashoshi a yankin a matsayin mataki na farko tun bayan da aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Disamba.
Duka bangarorin biyu wato na gwamnati da kuma na Houthi sun cimma yarjejeniyar barin tashar jirgin ruwan domin bayar da dama don shigo da kayayyakin tallafi.
A kalla fararen hula 6,800 aka kashe a yakin basasar Yemen wanda aka shafe shekaru hudu ana gwabzawa.
Hakazalika yakin ya yi sanadiyar jikkata mutum 10,700 kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana, yayin da dubban mutane suka mutu sakamakon rashin samun ingantaccen abinci mai gina jiki da kuma cututtuka da rashin lafiya iri-iri.