Liverpool ta yi rashin nasara da ci 1-0 a Atletico Madrid a wasan zagaye na biyu a gasar cin kofin Zakarun Turai da sukka fafata ranar Talata.
Atleticon ta ci kwallon ne a minti hudu da fara wasa ta hannun Saul Niguez.
Ita kuwa Borussia Dortmund ta yi nasara ne a kan Paris St-Germain da ci 2-1 a karawar da suka yi a Jamus.
Kungiyoyin sun buga minti 45 babu ci, illa hare-hare da suka dunga kai wa junansu.
Sai bayan da suka koma zagaye na biyu ne Dortmund ta ci kwallo ta hannun Erling Haaland daga baya minti shida tsakani Neymar Da Silva ya farke.
Daga baya ne Dortmund ta kara na biyu ta Erling Haaland ya kara na biyu.

