An cafke ‘yan sanda biyar bisa zargin kisan kai a Amurka

,

Rundunar ‘yan sanda ta birnin Memphis da ke Murka ta kama jami’anta biyar bisa zargin kashe Tyre Nichols, tare da soke rundunarta ta musamman mai yaÆ™i da laifukan kan titi ta ‘Scorpion’ domin maido da zaman lafiya a unguwanni, wanda aka zargi jami’anta da haddasa mutuwarsa.

Rundunar mai jami’ar 50 an É—ora mata alhakin yaÆ™i da muyagun laifuka a wasu sassan birnin.

To sai dai yanzu an soke rundunar bayan da aka ga jami’anta a wani bidiyo suna dukan Mista Nichols mai shekara 29, ranar 7 ga watan Janairu.

A wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan birnin ta fitar ta ce ”ta yanke shawarar soke rundunar gaba É—aya ne domin martaba rundunar.

Iyalan mista Nichols sun yi maraba da wannan matakin a wata sanarwa da suka fitar ta hannun lauyansu, suna masu kira ga hukumomi da su yi abin da ya dace domin hukunta mutanen da ake zargi da aikata kisan gillar kan mista Nichols, domin yi wa al’ummar Memphis adalci.

A watan Oktoban 2021 ne aka Æ™addamar da rundunar domin yaÆ™i da aikata munanan laifuka, kamar satar mota da ayyuka masu alaÆ™a da ‘yan daba.

Tuni dai aka kori jami’an ‘yan sandan biyar waÉ—anda aka samu da laifin kisan na makon da ya gabata.

An kuma gabatar da su a gaban kotu ranar Alhamis inda aka tuhume su da laifin kisan kai, da wasu laifuka masu alaƙa da kisan gilla.

To sai dai lauyoyin biyu daga cikin jami’an sun ce jami’an ba su amince da laifin ba.

ÆŠaruruwan masu zanga-zanga ne da suka taru a harabar shalkwatar rundunar ‘yan sandan birnin Memphis suna neman sauyi a rundunar ‘yan sandan wanda suka ce tana aikata zalunci a birnin da ma Æ™asar baki É—aya.

”An soke rundunar da ta kashe Tyre”, in ji wani mai zanga-zanga da yake magana da tarho a taron jama’ar waÉ—anda suka tsinke da sowa.

A zantawarta da BBC ranar Juma’a shugabar ‘yan sandan birnin CJ Davis ta ce an samar da rundunar ‘Scorpion’ ne domin magance laifukan ‘yan bindiga daÉ—i a birnin.

To amma ta yarda cewa jami’an rundunar da suka kashe Tyre Nichols sun aikata zalunci.

”Muna auna ayyukan duka rundunonin da ke Æ™arÆ™ashinmu” in ji ta.

”Wannan mataki ne da ya wajaba mu É—auka. muna buÆ™atar yin ayyukanmu a buÉ—e ga jama’a”.

Da farko ‘yan sanda sun ce sun tsayar da mista Nichols ne kan zarginsa da tuÆ™in ganganci, wanda kuma ba a tabbatar ba.

Ya mutu ne ranar 10 ga watan Janairu, a asibiti kwanaki uku bayan dukan da ya sha a hannun ‘yan sandan.

Kamar sauran jami’an ‘yan sandan biyar da ake zargi shi ma mista Nichols baÆ™ar fata ne.

Rundunar ‘yan sandan ta saki wasu bidiyoyi huÉ—u da aka naÉ—a daga wuraren tsayar da ababen hawa bayan faruwar lamarin ranar Juma’a, wanÉ—anda tsawonsu ya kai sa’a guda.

Asalin hoton, Reuters

Bayan sakin bidiyoyin ne kuma aka ƙaddamar da zanga-zangar lumana a birnin, inda wasu masu zanga-zangar suka toshe manyan titunan birnin, bayan wasu da aka samu a wasu wurare a faɗin ƙasar.

Da yawa daga cikin masu zanga-zangar na riÆ™e da kwalaye suna neman a yi wa mista Nichols adalci, da kuma kawar da zaluncin ‘yan sanda.

Magajin garin birnin Memphis ya ce daga watan Oktoban 2021 zuwa Janairun 2022, rundunar ta kama mutum 566, da ƙwace wa mutane tsabar kuɗin da suka kai dala 100,000 tare da ababane hawa 270 da makamai 253.

ÆŠaya daga cikin jami’an da aka kama kan zargin kashe mista Nichols an taÉ“a kai shi Æ™ara bayan da wani mutum ya zarge shi da dukansa a lokacin da yake fursuna shekara takwas da suka gabata.

More News

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...

An fara rushe wasu gine-gine 500 a kasuwar Karmo dake Abuja

Hukumar FCTA dake kula da birnin tarayya Abuja ta fara rushe gine-gine sama da 500 da aka yi ba bisa ka'ida ba a kasuwar...

Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa

A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa, a ziyarar da Faye ya...

NEMA ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo dasu gida daga ƙasar Chad

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta ce ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo da su bayan da su ka maƙale...