Fadar shugaban ƙasa ta ce ma’aikatar aikin gona da wadata ƙasa da abinci tana kan matakin karshe na fara sakin hatsi metric tan 42000 ga ƴan ƙasa masu ƙaramin ƙarfi.
Bayo Onanuga mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin sadarwa da tsare-tsare shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar.
Onanuga yace hatsin dake rumbuna daban-daban a wurare 7 ana saka su a sabon buhu kafin a miƙa su ga hukumar bada agajin gaggawa ta ƙasa NEMA.
“Buƙatar saka hatsin a buhu shi ne ya kawo tsaikon saboda buhunan sababbi ne gwamnati ta sayo su,” ya ce
“Ƴan Najeriya basa buƙatar su biya kuɗin hatsin saboda kyauta ne,”
Da yake magana kan batun ministan ma’aikatar gona, Abubakar Kyari ya ce sanarwar shirin fitar da hatsin ya haifar da faduwar farashin kayan abinci a kasuwanni.