An bayyana dalilin da yasa ba a fara rabon kayan abincin da gwamnatin tarayya za ta raba ba

Fadar shugaban Æ™asa ta ce ma’aikatar aikin gona da wadata Æ™asa da abinci tana kan matakin karshe na fara sakin hatsi metric tan 42000  ga Æ´an Æ™asa masu Æ™aramin Æ™arfi.

Bayo Onanuga mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin sadarwa da tsare-tsare shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar.

Onanuga yace hatsin dake rumbuna daban-daban a wurare 7 ana saka su a sabon buhu kafin a miƙa su ga hukumar bada agajin gaggawa ta ƙasa NEMA.

“BuÆ™atar saka hatsin a buhu shi ne ya kawo tsaikon saboda buhunan sababbi ne gwamnati ta sayo su,” ya ce

“Ƴan Najeriya basa buÆ™atar su biya kuÉ—in hatsin saboda kyauta ne,”

Da yake magana kan batun ministan ma’aikatar gona, Abubakar Kyari ya ce sanarwar shirin fitar da hatsin ya haifar da faduwar farashin kayan abinci a kasuwanni.

More News

Mutane 11 Sun Mutu A Wani Hatsarin Mota A Kano

Mutanen da basu gaza 11 ne ba aka tabbatar da sun mutu a yayin da wasu 16 suka jikkata mutum É—aya kuma ya tsira...

Ƙasar Amurika ta fara shirin kwashe sojojinta daga Nijar

Gwamnatin kasar Amurka ta fara shirin janye dakarunta daga jamhuriyar Nijar kamar yadda kafar yaÉ—a labarai ta CBS ta bada rahoto. Wani jami'in ma'aikatar wajen...

Sojoji sun kashe Æ´an ta’adda biyu tare da gano makamai a jihar Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun kashe wasu ƴan ta'adda biyu a ƙauyen Kana dake ƙaramar hukumar Biu ta jihar Borno. A wata sanarwa ranar Asabar...

An halaka mutane 6 a wani faÉ—a tsakanin Æ´anbindiga da Æ´anbanga

Mutane 6 ne suka rasa rayukansu a wata arangama da aka yi tsakanin ‘yan bindiga da ’yan banga da aka fi sani da ‘Yan...