
Biyo bayan cika sharuɗan da kotu ta gindaya masa a yanzu haka shahararren mawakin nan dan gidan Fela, Seun Kuti ya koma gida inda ya haɗu da iyalinsa bayan shafe kwanaki da yayi a hannun ƴan sanda a tsare.
A ranar Talata ne mawakin ya bar ofishin yan sanda na Panti dake Ikeja.
Tun da farko lauyoyinsa da suka haɗa da Adeyinka Olumide-Fusika, SAN, da Kunle Adegoke, SAN sun bayyana cewa tuni ya cika dukkan sharuɗan belin da aka gindaya masa.
An kama Seun ne bayan da wani fefan bidiyo ya bayyana inda a ciki aka ganshi yana marin wani jami’in ɗan sanda abin da ya jawo babban sufeton ƴan sanda bayar da umarnin a kamo shi a duk inda yake.