An bawa Ganduje da matarsa sarautar gargajiya a Ibadan

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da maidakinsa, Hafsat Abdullahi Umar sun samu sarautar gargajiya daga masarautar Ibadan ta jihar Oyo.

Olubadan, Dr. Lekan Balogun shi ne ya jagoranci bikin nadin sarautar a wani kasaitaccen biki da aka gudanar ranar Asabar a Ibadan.

An DAI nada Ganduje sarautar Aare Fiwajoye yayin da maidakinsa kuma aka bata sarautar Yeye Aare Fiwajoye.

Manyan bakin da suka halarci wurin taron sun hada da Bola Ahmad Tinubu dan takarar shugaban kasa a jam’iyar APC.

More News

Mayakan Boko Haram 314 sun mika wuya ga sojoji a Bama

Rundunar sojan Najeriya na cigaba da samun gagarumar nasara a yakin da take da mayakan Boko Haram.. A sakamakon kakkauta farmaki da hare-hare da rundunar...

Mayakan Boko Haram 314 sun mika wuya ga sojoji a Bama

Rundunar sojan Najeriya na cigaba da samun gagarumar nasara a yakin da take da mayakan Boko Haram.. A sakamakon kakkauta farmaki da hare-hare da rundunar...

An ɗage sauraron shari’ar Hadizan Gabon

Khadi Rilawanu Kyaudai na kotun shari'ar musulunci dake zamanta a Magajin Gari Zariya,ya dage shari'ar da yake sauraro tsakanin yar wasan Kannywood, Hadiza Gabon...

Buhari ya rantsar da sabon Alkalin Alkalai

Shugaban kasa, Muhammad Buhari ya rantsar da mai shari'a, Olukayode Ariwoola a matsayin, babban Alkalin Alkalai na Najeriya. Hakan na zuwa ne biyo bayan murabus...