An ƙona ofishin hukumar zaɓen jihar Akwa Ibom

Wasu ɓatagari da ake kyautata zaton ƴan bangar siyasa ne sun ƙona ofishin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Akwa Ibom dake ƙaramar hakumar Ibiatuk Ibiono a jihar.

Mutanen sun aikata haka ne a dai-dai lokacin da ake gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi 31 dake faɗin jihar.

Da ta ke tabbatar da faruwar lamarin a ranar Asabar, Timfon John mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Akwa Ibom ta ce ba a samu asarar rayuka ba  kuma gobarar bata shafi kayayyakin zaɓe ba.

John ya ƙara da cewa na cigaba da yin bakin ƙoƙarinta wajen ganin an kama tare da hukunta waɗanda suka aikata laifin.

Ta tabbatarwa da ƴan Najeriya cewa zaɓen na cigaba da gudana yadda lami lafiya a kamar yadda aka saba.was

More News

TCN na ci gaba da ƙoƙarin gyaran wutar lantarkin da ta lalace kwana biyu

Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya sanar da ci gaban da aka samu wajen farfado da rukunin wutar kasa bayan wata tangardar...

Magoya bayan jam’iyyar NNPP sun ƙona jar hula

Wasu daga cikin mambobin wani tsagi na jam'iyar NNPP sun barranta kansu da jagoran jam'iyar na ƙasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso inda suka riƙa...

PDP ta ɗauki hanyar warware rikicin jam’iyyar

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad ya ce  an kawo karshen rikicin cikin gida da ya dabaibaye jami'yar PDP. Mohammed wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin...

Dakarun Najeriya sun cafke wasu ƴan’aiken ƴanbindiga a Kaduna

Sojoji sun kama wasu mutum biyu da ake zargi da kaiwa 'yan bindiga sakonninsu a kasuwar ƙauyen SCC da ke ƙaramar hukumar Kachia a...