An ƙona gidaje da dama a garin da aka kashe sojoji 16 A jihar Delta

Gidaje da dama ne dake garin Okuoma a gaɓar ruwa aka ƙone ƙasa da sa’o’i 24 da kisan sojoji 16 a garin bayan da suka je kwantar da wani rikicin kabilanci.

Tukur Gusau daraktan yaɗa labarai a ma’aikatar tsaron ƙasa a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar ya ce sojojin da suka haɗa Laftanal Kanal, Manjo 2   Kaftin guda ɗaya da kuma  wasu sojoji 12 wasu matasa ne suka kashe su a ranar Alhamis.

Sojojin sun je garin ne biyo bayan kiran kai ɗaukin gaggawa da aka yi masu sakamakon rikicin kabilanci tsakanin garuruwan Okuoma da Okoloba a jihar Delta.

Tuni babban hafsan hafsosin sojan  Najeriya, Christopher Musa ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan kisan.

A wani hoton bidiyo da gidan Talabijin na Channels ya wallafa ya nuna wasu gidaje dake garin suna ci da wuta.

Tuni mazauna garin da dama suka tsere saboda fargabar ramuwar gayya daga sojojin.

More from this stream

Recomended