Wata kotu a Jihar Legas da ke Ikeja ta yanke wa wani mutum mai suna Onyeka Mbaka daurin zuwa gidan yari bisa zargin lalata da wata yarinya ‘yar shekara 15.
Alkali mai shari’a Rahman Oshodi ne ya bayar da umurnin a ci gaba da tsare wanda ake kara bayan an gurfanar da shi a gaban kuliya bisa wannan tuhuma a kansa.
Lauyan mai gabatar da kara, Mis Bukola Okeowo, ta shaida wa kotun cewa wanda ake tuhumar ya bata sunan wacce aka cutar a wani lokaci.
Okeowo ta ce lamarin ya faru ne a lamba 16, titin Moshalasi, a yankin Ilasa na jihar.
Ta ce wanda ake tuhumar ya yi lalata