Amurkawa sama da dubu hamsin sun kamu da korona a kwana 1

Getty Images

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Sabbin alƙaluman masu kamuwa da cutar korona a Amurka ya yi matuƙar tashin gwauron zabbi inda ya zarta mutum dubu hamsin a cikin kwana guda.

Cutar ta harbi kusan mutum dubu goma a jihar Califonia kadai, abin da ya sa mahukuntan jihar sake ɓullo da wasu matakan daƙile annobar da aka janye a baya.

Lamarin na zuwa ne kwana guda bayan babban likitan da ke jagorantar yaƙi da korona a Amurka Dr Anthony Fauchi, ya yi gargadin cewa yawan masu kamuwa zai iya haura dubu ɗari a cikin kwana ɗaya.

Tuni dai gwamnan Califonia, Gavin Newsom, ya sake bijiro da wasu ɓangarori na matakan kulle, bayan sannu a hankali an riƙa sassauta su a jihar.

Matakan sun haɗar da haramta cin abinci a gidajen sayar da abinci, da zuwa sinimu, da kantunan barasa da gidajen adana kayan tarihi tsawon a ƙalla mako uku.

Gwamna Newsom ya sake Æ™aÆ™aba matakan ne gabanin hutun ranar 4 ga watan Yuli, lokaicn da jami’ai ke fargabar samun Æ™arin yaÉ—uwar cutar.

Wasu mazaunan birnin Los Angeles kamar Marisol Martinez sun yi imani matakin yana kan hanya.

Ta ce “Abin takaici ne sake buÉ—e birnin nan, Ina jin hakan ya É—an yi wuri. Kowa kawai yana ta fitarsa, suna zuwa kantunan barasa, suna zuwa taruka, suna zuwa gidajen abinci.

Shi ma Ben Smith ya faÉ—a wa BBC cewa: “Tabbas akwai wasu yankunan Califonia da mutane ba sa nuna damuwa game da halin da ake ciki”.

A cewarsa ba za ka ga mutane na sa takunkumi ba, ba za ka ga mutane na zama nesa-nesa da juna ba.

“Ko da yake ina jin a yankin Los Angeles mutane suna matuÆ™ar yin abin da ya dace kuma mutane na Æ™oÆ™arin zama cikin hattara yadda ya kamata musammam ma a yanzu da lamarin ke Æ™ara Æ™azancewa, alÆ™aluma ke ci gaba da hauhawa,” in ji shi

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...