Amurka ta sayar wa Kuwait makaman yaki na $1.425 bn

Hakkin mallakar hoto
ARLOMAGICMAN/GETTY IMAGES
Image caption

Kuwait City, babban birnin kasar Kuwait

Amurka za ta sayar wa Kuwait makamai masu linzami samfurin Patriot guda 84 tare da wasu makaman da za su kare kasar daga hare-hare daga kasashe irin su Iran kan kudi dala biliyan 1.425.

A wata sanarwa, ma’aikatar harkokin waje ta Amurka ta ce cinikin zai zama mai amfani ga kasashen biyu:

“Wannan cinikin da aka shirya yi zai taimaka wa manufar hulda da kasashen waje da tabbatar da tsaron Amurka ta hanyar taimaka wa wata babbar kawa da ba ta cikin kungiyar tsaro ta NATO, wadda muhummiyar kasa ce da ka iya tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

  • An ceto matan Najeriya da aka yi safarar su zuwa Lebanon
  • Iran: Sojojin Iran 19 sun mutu a Tekun Oman yayin atasayen soji

Sanarwar ta kuma ce: “Wannan cinikin zai inganta tsaron kasar Kuwait da muradunta na yau da na gobe, musamman a banagaren kare albarkatunta na mai da makamashi.

Wannan shagube ne ga hare-haren da aka kai wa wasu sansanonin hako mai da tace shi a Saudiyya a watan Satumbar bara wanda aka dora alhakinsa kan Iran.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Image caption

Amfanin makamin Patriot shi ne kare kasa daga hari daga makamai masu linzami

An raba cinikin gida uku ne, inda kashin farko wani kamfani mai kera kayan yaki, Lockheed Martin zai samar da makaman roka masu linzami na dala miliyan 800.

Sai kuma kwangilar horar da dakarun Kuwait da ba su tallafi da kamfanin na Lockheed Martin tare da kamfanin Raytheon za su yi na dala miliyan 425.

Akwai kuma wata kwangilar ta uku da kamfanonin biyu za su gudanar da kudinta ya kai dala miliyan 200 da za su gyara tsofaffin makaman yakin kasar ta Kuwait.

More News

An kori sojojin da suka kashe wani jami’in NDLEA a Neja

Rundunar sojin Najeriya ta gurfanar tare da korar wasu sojoji shida da ake zargi da hannu a mutuwar wani jami’in hukumar NDLEA, Kingsley Chimetalo,...

Maniyyayan Najeriya sama da 18,000 sun isa Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce adadin maniyyata 18,906 na shekarar 2024/1445 aka yi jigilarsu zuwa kasar Saudiyya.Hukumar ta bayyana hakan ne a rana...

Talauci ko rashin wadata ba dalili ne na ƙazanta ba

Daga Aliyu M. AhmadBa tilas sai ka sanya manyan shadda ko yadi ba, ka ɗinka daidai da kai, kilaritarka ta sha gugar charcoal. Sutura...

Ƴan sanda sun kama wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a Kaduna

Jami'an ƴan sanda sun samu nasarar kama wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a jihar Kaduna. Mutumin da aka kama mai suna, Muhammad Bello ɗan...