Amnesty Int′l ta zargi jami′an tsaron Najeriya | Labarai

Kungiyar Amnesty Int’l, ta zargi jami’an tsaron Najeriya da amfani da karfi fiye da kima a kan fararen hula masu neman ballewa a yankin kudu maso gabashin kasar.
Kungiyar ta Amnesty ta kuma yi zargin jami’an sun kashe akalla mutane 115.
Sai dai rikicin da ya taso jihohin ‘yan kabilar Igbo a bana, ya yi sanadin salwantar jami’an ‘yan sanda 127 a cewar ‘yan sandan.
Akwai ma wasu ofisoshin ‘yan sanda 20 da na hukumar zabe da aka lalata, kamar yadda kafofin watsa labaran cikin Najeriyar suka tabbatar.
An dai zargi kungiyar IPOB mai rajin kafa kasar Biafra ta Igbo zalla da kuma wata Eastern Security Network, ESN, a takaice da aikata aika-aikar. Amma kungiyar IPOB ta Nnamdi Kanu, ta musanta zarge-zargen.
Amnesty Int’l dai ta dora alhakin kashe-kashen fararen hulan ne a kan ‘yan sanda da kuma jami’an DSS.

More from this stream

Recomended