Amina Amal Ta Kwanta Jinya Bayan Ta Sha Duka A Hannun Hadiza Gabon

Jaruma Amina Amal ta kwanta rashin lafiya bayan dukan da kawo wuka da fitacciyar Jaruma Hadiza Gabon ta yi ma ta tare da taimakon wasu karti maza.

Majiyar LEADERSHIP A YAU ta tabbatar da cewa, a yanzu haka yarinyar ta na fama da yanayi na rashin lafiya da kuma rudewa sakamakon mumman tashin hankalin da ta fuskanta tun a daren farko da Jaruma Gabon da tawagarta su ka far ma ta a gidanta da ke Kaduna.

Idan za a iya tunawa, Amal ta dora wani hotonta ne a Instagram wanda ke nuna cibiyarta a waje, lamarin da janyo zafafan martani daga masu yin sharhi a kan hoton, ciki har da wasu daga cikin ‘yan fim, kamar ita Gabon da Jaruma Aisha Tsamiya da
Darakta Hassan Giggs da sauransu.

To, amma abin mamaki shi ne Gabon ce kadai wacce Amal ta mayar wa da martani ta hanyar yin shagube kan dabi’a ta madigo, lamarin da ya fusata Gabon din.

Majiya mai tushe ta labarta wa wakilinmu cewa, sau uku ‘yan tawagar sun hada da maza kamar guda biyar ko shida, wadanda wasunsu a motar Hadiza Gabon din su ke yayin da wasu kuma su ke cikin babur din Adaidaita Sahu, cikinsu har da wasu fitattun ‘yan fim guda biyu; daya darakta ne ma.

More News

Mutane 11 Sun Mutu A Wani Hatsarin Mota A Kano

Mutanen da basu gaza 11 ne ba aka tabbatar da sun mutu a yayin da wasu 16 suka jikkata mutum É—aya kuma ya tsira...

Ƙasar Amurika ta fara shirin kwashe sojojinta daga Nijar

Gwamnatin kasar Amurka ta fara shirin janye dakarunta daga jamhuriyar Nijar kamar yadda kafar yaÉ—a labarai ta CBS ta bada rahoto. Wani jami'in ma'aikatar wajen...

Sojoji sun kashe Æ´an ta’adda biyu tare da gano makamai a jihar Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun kashe wasu ƴan ta'adda biyu a ƙauyen Kana dake ƙaramar hukumar Biu ta jihar Borno. A wata sanarwa ranar Asabar...

An halaka mutane 6 a wani faÉ—a tsakanin Æ´anbindiga da Æ´anbanga

Mutane 6 ne suka rasa rayukansu a wata arangama da aka yi tsakanin ‘yan bindiga da ’yan banga da aka fi sani da ‘Yan...