Kasa da sa’o’i 24 kafin karewar wa’adin mulkinsa, gwamnan jihar Lagos mai barin gado, Akinwumi Ambode ya mika ragamar mulkin jihar ga gwamna mai jiran gado,Babajide Sanwo-Olu da kuma mataimakinsa Obafemi Hamzat a wani taron sirri da ya gudana a gidan gwamnatin jihar na Alausa dake Ikeja.
A wani taron manema labarai da ya gudanar bayan ganawar da yan jaridar dake gidan gwamnatin jihar,zababben gwamnan jihar ya ce Ambode ya bashi shawarwari masu muhimmanci da kuma wani kundin bayanai dake dauke da bayani kan nasarori da kuma akasin haka a shekara hudu da ya shafe yana mulkin jihar.
Gwamna Akinwumi Ambode ya rasa tikitin takara a jam’iyar APC bayan da ya raba gari da jagoran jam’iyar APC na kasa,Bola Ahmad Tinubu.