Ambaliyar ruwa ta sake lalata wani sashe na babbar hanyar Kano zuwa Maiduguri

Ambaliyar ta lalata babbar hanyar Kano zuwa Maiduguri a tsakanin a garin Azare zuwa Jama’are a jihar Bauchi.

Hakan na zuwa ne ƙasa da mako biyu bayan da ambaliyar ruwan ta lalata wani sashe na titin Kano zuwa Maiduguri a tsakanin garin Azare zuwa Bulkachuwa.

Da yake duba wurin da ya lalace a wata ziyara da ya kai ranar Alhamis da ya kai gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad ya ce tuni ya sanar ministan ayyuka, Dave Umahi kan halin da ake ciki.

Gwamnan ya yi gargaɗin cewa al’ummomin  dake yankin na fuskantar ambaliyar da zata shanye muhallansu matukar ba a shawo kan ruwan da yake malala ba.

A cikin watan Afrilu ne gwamnatin tarayya tayi gargaɗin cewa ƙanana hukumomi 148 dake jihohi 34 za su fuskanci ambaliyar ruwa a daminar bana.

More from this stream

Recomended