Ambaliyar ruwa ta raba mutane da dama da gidajensu a Kaduna

[ad_1]








Ruwan sama ba kakkautawa ya raba daruruwan mutane da gidajensu a wasu unguwanni dake wajen birnin Kaduna.

Gidaje da dama ne suka shafe sakamakon ruwan saman da ya fara da yammacin ranar Alhamis ya kuma tsaya da safiyar ranar Juma’a.

Unguwannin da masifar ambaliyar ruwan tafi ƙamari sun hada da, Unguwar Rimi,Bachama Road, Barnawa, Kudenda, Kawo, Gonin Gora da sauransu.

Hakan ya sa mutane da dama sun nemi mafaka a makarantu da kuma coci-coci.

Ambaliyar ta faru ne yan kwanaki bayan gargadi daga hukumar agajin gaggawa ta jihar Kaduna(SEMA) da kuma hukumar kare muhalli ta jihar Kaduna (KEPA) akan yiyuwar faruwar ambaliyar ruwa.

Hukumomin biyu sun yi gargadin yiyuwar faruwar ambaliyar ruwa musamman masu gidaje a kusa da bakin Kogin Kaduna da kuma mazauna kusa da hanyar ruwa.

Anyi ta maimaita gargadin hukumomin biyu a gidajen rediyo.

A wasu daga cikin unguwanni da abin ya shafa anga mazauna yankin suna kwashe kayayyakinsu zuwa gidan yan’uwansu dake makotan unguwanni.

Wasu daga cikin magidantan sun bayyana cewa basu da masaniya akan gargadin.




[ad_2]

More News

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...

An fara rushe wasu gine-gine 500 a kasuwar Karmo dake Abuja

Hukumar FCTA dake kula da birnin tarayya Abuja ta fara rushe gine-gine sama da 500 da aka yi ba bisa ka'ida ba a kasuwar...

Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa

A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa, a ziyarar da Faye ya...

NEMA ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo dasu gida daga ƙasar Chad

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta ce ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo da su bayan da su ka maƙale...