Ambaliyar Ruwa Ta Mamaye Wani Rukunin Gidaje Dake Abuja

Adadin mutanen da kawo yanzu ba a iya tantance yawansu ba ne suka maƙale a gidajensu dake rukunin gidaje na Trade Moore dake Lugbe a Abuja sakamakon ambaliyar ruwa da ruwan sama mai yawa da aka yi ya haifar.

Faya-fayan bidiyo da suka karaɗe intanet sun nuna yadda gidaje da kuma motoci suka nutse a ruwa.

A wani rahoto da ta fitar kan halin da ake ciki hukumar bada agajin gaggawa ta kasa, NEMA ta ce wani direba matukin wata mota kirar Peugeot 406 mai namba YLA 681 FS ya nutse a ruwan kuma ana cigaba da neman sa.

“An ceto mutane huɗu kuma suna cikin hayyacinsu” a cewar sanarwar.

More from this stream

Recomended