Ambaliya ta shafi sama da mutum 33,000 a Najeriya

A shekarar 2023, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta bayyana cewa sama da mutane 33,000 ne ambaliyar ruwa ta shafa a jihohi goma na Najeriya.

Daraktar Tsare-tsare, Bincike da Hasashen NEMA, Hajiya Fatima Kasim, ta bayyana haka a wajen taron hadin gwiwa na gaggawa, ranar Alhamis a Abuja.

A cewar NEMA, abubuwan da ke haifar da ambaliyar ruwa a kowace shekara sun hada da rashin isassun gine-gine da tsarin gine-gine, rashin tsarin magudanar ruwa, rashin kula da sharar gida, da ayyuka masu cutarwa kamar sare bishiyoyi da sauyin yanayi.

Har ila yau, Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen za a samu ruwan sama wanda ya fi yadda aka saba a bana, lamarin da ke janyo yawaitar ambaliya a kananan hukumomi 178 da ke fadin jihohi 32 da kuma babban birnin tarayya (FCT).

More from this stream

Recomended