Almajiranci: Gwamnatin Yobe za ta inganta tsarin

Yobe

Hakkin mallakar hoto
Facebook/Hon Mai Mala Buni

Kwamitin da Gwamnan Yobe a Najeriya Mai Mala Buni ya kafa domin yi wa almajiranci kwaskwarima ya ce yana tuntubar malaman addinin Musulunci don ganin an gyara tsarin don dacewa da zamani.

Sai dai wannan mataki na gwamna Mai Mala Buni na zuwa ne yayin da wasu jihohi kamar Kano ke kokarin soke almajiranci a jihohinsu.

Batun almajiranci dai ya dade yana ci wa akasarin jihohin arewa tuwo a kwarya inda da dama daga cikin gwamnatocin yankin ke kokarin samar da maslaha.

Dr Muhammad Sani Idris, shugaban kwamitin da gwamnan na Yobe ya kafa ya ce ya zuwa yanzu, sun ganawa da Sheikh Dahiru Usman Bauchi inda suka yi masa bayanin kudurce-kudurcen gwamnatin Yobe da bukatarsu ta gwamnati ta shigo lamarin.

A cewarsa, Sheikh Dahiru Bauchi ya yi maraba da batun inda ya bayyana musu cewa hakan shi ne zai kawo ci gaba a al’amuran kasa.

“Mun je wajen Sheikh Ibrahim Saleh babban malami ne da duk duniya ta san shi kuma ya ce ba abin mamaki ba ne a ce wannan ya zo daga gwamnan Yobe saboda shi jika ne na manyan malaman Gazargamu.”

A cewarsa, “al’amarin karatu da samun dabaru dole ne mutane sai sun mike hannayensu sun kuma tattauna da mutane da dama, matsayin gwamnatin Kano (na haramta almajiranci) daban, matsayin neman karin bayani wajen mutanen da yake sune masana wannan al’amarin daban.”

Game da batun hana almajiranci, Dr Sani Idris wanda shi ne kwamishinan ilimi a jihar ta Yobe ya ce: “mu a jihar Yobe, mu ba alkalai ba ne, ba aikinmu ne mu gane wane ya yi dai dai wane bai yi daidai ba, Mu abin da muke gani yana da kyau shi ne mu tsayawa Al’Qurani mu zo da wani tsari.”

“Gwamna ya ce lallai mu kar mu damu da abin da wani ya yi mu damu da abin da muke son mu yi, idan muka yi abin namu idan ya zamana mai kyau ne watakila abin namu zai amfanar da wani, wanda kuma yake da wani tsari bamu da tilas a kan kowa.” in ji Dr Sani Idris.

An dai sha gudanar da bincike da nazarce-nazarce da dama gami da ba da shawarwari kan yadda za a magance matsalar bara, musamman a arewacin Najeriya.

Ko a 2014 wani kwamitin wasu fitattun mutane da suka shafe wata takwas suna yi wa gwamnonin arewa nazari kan wasu matsaloli musamman na bara, sun gabatar da rahoto kan yadda za a magance su.

Sai dai sama da shekara biyar da mika wa gwamnonin wannan rahoto, za a iya cewa ba a ga sauyi ba.

More News

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...

An fara rushe wasu gine-gine 500 a kasuwar Karmo dake Abuja

Hukumar FCTA dake kula da birnin tarayya Abuja ta fara rushe gine-gine sama da 500 da aka yi ba bisa ka'ida ba a kasuwar...

Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa

A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa, a ziyarar da Faye ya...

NEMA ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo dasu gida daga ƙasar Chad

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta ce ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo da su bayan da su ka maƙale...