Alkalin wasa ya busa tashi a minti na 89

Wasan da aka buga tsakanin kasar Mali da Tunisia a gasar cin Kofin Kasashen Nahiyar Afrika ya bar baya da kura bayan da alkalin wasa Janny Sikazwe ya tashi wasan a minti na 89.


Kasar Mali ce ta doke Tunisia da ci 1 da nema ta hanyar bugun saga kai sai mai tsaron gida.
Tun da farko alkalin wasan ya busa tashi a minti na 85 inda aka ankarar da shi cewa lokaci bai cikaba daganan aka cigaba da wasan amma kuma ya sake busa tashi a minti na 89.


Bayan shafe minti 40 ana tataburza wakilan hukumar Kwalllon Kafa ta Nahiyar Africa CAF sun bukaci a kara mintuna 4 amma tawagar yan wasan kasar Tunisia suka ki yarda su dawo a cigaba.

More News

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...

Delta: An dawo da gawarwakin sojojin da aka kashe Abuja don yi musu jana’iza

Gawarwakin sojojin da aka kashe a jihar Delta kwanan nan sun isa maƙabartar sojoji ta kasa da ke Abuja. Gawarwakin sun iso ne da misalin...