
Kotun koli ta tabbatar da gwamnan jihar Neja, Sani Bello
Dukkan alkalan guda bakwai sun amince cewa laifin lauyoyin jam’iyyar ne da ba su yi wa ‘yan jam’iyyar bayani ba dangane da rashin hurumin karar da suka shigar a gaban kotun ta koli.
Jam’iyyar APC a jihar Taraba dai ba ta da dan takarar gwamna a saboda haka ne alkalan suka ce “laifin lauyoyin ne da ba su gamsar da jam’iyyar ba cewa ba ta bukatar daukaka kara.”
Su kuma lauyoyin jam’iyyar ta APC a jihar Abia sun gaza gabatar da shaidu a gaban kotu inda suka jibge tarin takardu agaban alkalan, al’amarin da ya sa kotun ta yi watsi da karar.
A ranar Laraba ne dai kotun Kolin kasar ta yi watsi da karar da dan takarar PDP Umar Nasko ya shigar gabanta inda ya kalubalanci nasarar da dan takarar APC Abubakar Sani Bello ya yi a zaben gwamna.
Kotun ta tabbatar da sahihancin zaben da aka yi da kuma gasgata hukuncin da kotun sauraren kararrakin zabe ta yi a baya kan zaben.
Har wa yau Kotun Kolin ta tabbatar da Darius Ishaku a matsayin gwamnan Taraba
Haka zalika kotun ta yi watsi da karar da aka shigar kan zaben Okezie Ikpeazu a matsayin gwamnan jihar Abia.
Kotun ta bayyana cewa ta amince da hukuncin da kotun sauraren kararrakin zaben ta yanke kan zaben Taraba inda ta ce jam’iyyar APC ba ta da dan takara a jihar a lokacin zabe.