Aljeriya: Za a kwato kudade daga waje

0
Tsohon shugaban Aljeriya Abdelaziz Bouteflika

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Zanga-zangar da ‘yan Aljeriya suka yi ta yi ce ta tilasta wa Abdelaziz Bouteflika mai shekara 82 sauka daga mulki

Daya daga cikin ‘yan kasar Aljeriya da suka hada kansu domin fafutukar kwato kudade da kadarorin daga kasashen waje, Lachemi Bolhecine wanda lauya ne da ke zaune a Switzerland,

ya ce kungiyar tasu ta kunshi kwararru 25.

Ya ce kusan dukkaninsu suna zaune ne a kasashe daban-daban, kuma sun kunshi lauyoyi da injiniyoyi da likitoci da masana tattalin arziki da sauransu.

Bolhecine ya ce tuni sun dukufa wajen neman gwamnatoci a kasashen Turai da Amurka da su dakatar da duk ire-iren kadarorin da suke zargi Mista Bouteflika da mukarrabansa sun mallaka ta hanyar wawure kudin jama’ar Aljeriya.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mista Bouteflika, ya kama mulkin Aljeriya tun 1999, kuma ya gamu da larurar shayewar jiki shekara shida da ta wuce

Lauyan ya ce a kiyasi dukiya ko kadadori da kudaden da suke wannan fafutuka ta neman dawo da su, sun kai na tsakanin dala biliyan 24 zuwa biliyan 60.

Amma kuma ya ce shi a matsayinsa na lauya yawan kudin ba shi ba ne abin da zai su wannan aiki.

Ya ce ko da kudaden ba su kai hakan ba, ko da dala dubu daya ce aka sace wa wani, a nan al’ummar Aljeriya ke nan, to akwai bukatar ya bi musu hakki har sai ya ga an dawo musu da kudin.

Sai an tabbatar an yi musu adalci, a kuma kiyaye da doka domin gaba.

Batun dai shi ne matakin farko gano kudaden, wanda kalubale ne shi kansa, kafin kuma a zo biybiyar gwamnatocin kasashe don ganin sun saki kudaden da kadarorin, wanda shi ma jan aiki ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here