Akpabio da Barau sun zama shugaba da mataimakin shugaban majalisar dattawa

Tsohon gwamnan Akwa Ibom sanata Godswill Akpabio ya zama sabon shugaban majalisar dattawa ta 10 da aka ƙaddamar a ranar Talata.

Akpabio ya kayar da babban abokin hamayyarsa sanata Abdulaziz Abubakar Yari.

Akpabio ya lashe zaben da aka gudanar a zauren majalisar da kuri’u 63 inda Yari ya samu kuri’a 46.

Har ila yau an zaɓi sanata Barau Jibrin ba tare da hamayya ba a matsayin mataimakin shugaban majalisar dattawa.

More from this stream

Recomended