Aikin hajji da musulmai kan yi a kowace shekara ya kai matuka a yau, inda mutane kimanin miliyan biyu da rabi suka taru a dutsen Arfa inda za su wuni suna addu’o’i tare da karatun alkur’ani.
Mahajjatan sun taru a kan wannan dutse da filin da ke makwaftaka da shi ne a gab da fitowar rana.
Wannan wuri na Arfa na da nisan kimanin kilomita 15 daga birnin Makka.
A wannan dutse ne dai annabi Muhammad (S.A.W) ya gabatar da hudubarsa ta karshe, wadda ake kira hudubar ban-kwana.
Aikin Hajji na daga cikin ginshikan muslunci guda biyar, wanda ake so musulmi ya aikata akalla sau daya a tsawon rayuwarsa.
Mahajjata dai na fitowa ne daga dukakkanin fadin duniya, to amma Indonesia wadda ita ce ta fi kowace kasa yawan musulmai a duniya, ita ce ta fi kowace yawan musulmai a wurin na aikin hajji.
Daya daga cikin darussan da aikin hajji ke koyarwa shi ne karfafa dangantaka, da kuma nuna cewa kowane dan’adam daidai yake a gaban Allah madaukaki.
A lokacin aikin dukkanin mahajjata kan sanya sutura iri wadda ake kira ihrami.