Ahmad Musa ya rage kudin mai a gidan mansa

Ɗan wasan Super Eagles, Ahmed Musa, ya sanar da rage farashin man fetur a gidan mansa, MYCA7 a Kano daga N620 zuwa N580 kowace lita.

Kwararren dan kwallon ya bayyana hakan ne a shafin sa na Twitter.

Musa ya rubuta: β€œFuel #580 @MYCA -7 Filling Station Kano. πŸƒβ€β™€οΈπŸƒβ€β™€οΈ,” abin da ya haifar da fara’a a tsakanin’yan Najeriya.

Wani mai amfani da Twitter, Scala @lakaas123, cikin zumudi ya tambaya β€œYaya Alhaji? N580 a Kano ba a Legas ba? Kuna yi mana rashi ne?” Sai Musa ya amsa da cewa, “Ni ne na yanke shawarar sayar da nawa a haka.”

More from this stream

Recomended