Shugaban majalisar dattawa ta 9, Ahmad Lawan ya ziyarci tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari dake mahaifarsa ta Daura.
Lawan wanda yake wakiltar shiyar Yobe North a majalisar dattawan ya isa gidan Buhari dake Daura da misalin ƙarfe 12:40 na rana inda ya samu kyakkyawar tarba daga tsohon shugaban kasar kamar yadda, Dr Ezrel Tabiowo mai ba shi shawara kan kafafen yada labarai ya bayyana.
A cikin sanarwar da Tabiowo ya fitar ta ce mutanen biyu sun tattauna kan batutuwa da dama amma kuma bai bayyana cewa ba ko batutuwan da suka tattauna na da alaka da zaɓen 2027.
A ƴan kwanakin nan ana cigaba da samun ƙaruwar ƴan siyasa dake cigaba da kai ziyara wurin tsohon shugaban ƙasa Buhari.
Tabiowo ya ce Lawan ya godewa Buhari kan shawarwarin da yake bayarwa da kuma irin shugabancin da ya yi daga shekarar 2015-2019.