Ahmad Lawan na so a yanke wa masu fyaɗe tsattsauran hukunci

Sanata Ahmad Lawan
Hakkin mallakar hoto
@DrAhmadLawan
Image caption

Sanata Ahmad Lawan ya ce tsauraran hukunci zai zama izina ga masu aikata laifin

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Ahmad Lawan ya bukaci mahukunta su rika yanke tsattsauran hukunci kan duk mutumin da aka samu da laifin fyade.

Ahmad Lawan ya yi kiran ne lokacin zaman Majalisar Dattawan na ranar Talata.
Sai dai bai bayyana abin da yake nufi da “tsattsauran hukunci” ba.
Yana kiran ne a daidai lokacin da ‘yan kasar suke Allah-wadai da fyaden da aka yi wa wasu mata a wurare daban-daban na kasar.
Daya daga cikinsu ita ce Vera Uwaila, wadda aka yi wa fyade a cikin coci a jihar Edo har ta mutu.
A cewar shugaban Majalisar Dattawan, “samun tsauraran dokoki na hukunta masu irin wannan laifi zai sa masu yin irin wannan ta’ada su daina”.

Abin da ya faru ga Vera Uwaila

Bayanai sun ce an yi wa Vera mai shekara 22 da ake kira Uwavera fyade a wata coci da ke kusa da jami’ar Benin a jihar Edo.
Batun dai ya ja hankali musamman a kafofin sadarwa na Intanet, inda aka ƙirƙiri maudu’in #JusticeForUwa wato tabbatar da adalci ga Uwa.
Tuni gwamnan jihar, Godwin Obseki ya umarci rundunar ƴan sandan jihar da ta gudanar da bincike da kuma hukunta duk wanda aka samu da hannu a al’amarin.
A ranar Laraba ne ɗalibar mai shekara 22 da ke nazarin ilimin ƙananan halittu ta je cocin Redeemed da ke kusa da jami’ar domin yin karatu kamar yadda ta saba yi, inda aka je aka same ta yashe a kasa jina-jina.
An dai ce an rotse kan Uwavera ne da tukunyar sinadarin kashe wuta bayan an yi mata fyaden.
Ƴar uwar marigayiyar, Judith Omozuwa ta shaida wa BBC cewa sai bayan kwana uku ne ta cika a asibiti.
“Da misalin karfe 6 na yamma ranar Asabar an kira babata daga coci cewa mu je ba su san abin da ya faru ga ‘yar uwata ba . Wata mace wadda ta samu ‘yar uwar tawa ta ce ta same ta kwance cikin jini kuma an yayyaga sikyat da dan kamfanta,” in ji ta.
Ta ƙara da cewa: “sun yi mata fyade, don ba ta taba sanin ɗa namiji ba. Ina matukar son ganin an samu waɗanda suka yi mata fyade domin a hukunta su.”
Sai dai Judith ta ce tuni sun kai maganar gaban ƴan sandan jihar, amma jami’an tsaron sun ce a fahimtarsu Uwavera ta rasu ne sakamakon rashin jituwarta da wasu zauna gari banza da ke unguwar Ikpoba Hill inda ta ke zaune.
Mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar ta Edo, DSP Chidi Nwabuzor ya shaida wa BBC cewa tuni suka fara bincike tun bayan da labarin yarinyar ya bazu a shafukan sada zumunta.
Lamarin dai ya ja hankalin ƴan Najeriya inda wasu suka yi Alla-wadai da batun musamman a shafukan sada zumunta, inda suke ta yin kiraye-kiraye ga gwamnatoci da duk masu ruwa da tsaki da a bi wa marigayiya Uwavera hakkinta domin ya zama izina ga masu son kwatanta irin haka a gaba.

More News

Tayoyin jirgin saman Max Air sun fashe a Yola

Jirgin saman kamfanin Max Air ƙirar Boeing 737 mai rijistar namba 5N-ADB dake ɗauke da fasinjoji 118 da ma'aikata 6 ya gamu da matsala...

Ɗan majalisar wakilai ta tarayya ya mutu

Hon. Olaide Akinremi Jagaba mamba a majalisar wakilai ta Najeriya dake wakiltar mazaɓar Ibadan North a majalisar ya mutu. Kawo yanzu babu cikakken bayani kan...

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...