Africom: Bukatar Buhari kan rundunar Amurka tamkar dawo da mulkin mallaka ne – Shehu Sani

Shehu Sanu ya ce muddin irin waÉ—anan rundunoni suka shigo fitarsu akwai wahala, domin maganar ta wuce na tsaro, za ta haifar da gasa ne tsakanin.

Asalin hoton, SHEHUSANI

Bayanan hoto,
Shehu Sanu ya ce muddin irin waÉ—anan rundunoni suka shigo fitarsu akwai wahala, domin maganar ta wuce na tsaro, za ta haifar da gasa ne tsakanin su

Tsohon É—an majalisar dattawan Najeriya Sanata Shehu Sani ya ce yana adawa da tsarin dawo da hedikwatar rundunar sojoji masu kula da Afirka wato AFRICOM zuwa nahiyar daga mazauninta da ke Jamus.

Sanata ya bayyana hakan ne bayan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga Amurka ta dawo da rundunar Afirka saboda matsaloli na tsaro.

Gwamnatin ƙasar ta ce kiran wani sauyin matsayi ne ga Najeriya wadda a baya ta riƙa nuna adawa kan yadda ƙasashen yamma ke kafa sansanoninsu a nahiyar Afirka.

Sai dai yanzu matsalolin tsaron da ake fama da su, sun sanya ganin fa’idar kawo rundunar sojojin ta Amurka.

Amma wasu ƴan adawa irinsu Shehu Sani sun ce kiran dawo da hedikwatar rundunar Amurkan ba mafita ba ce, don kuwa matakin zai iya buɗe ƙofa ga wani sabon salon mulkin mallaka da kawo sojojin ƙasashen yamma su zo su karkasa ƙasashe.

‘Rundunonin Æ™etare ba su ne mafita ba’

Sanatan ya ce da zarar an buÉ—e irin wannan Æ™ofa to su ma sauran rundunonin Æ™asashen masu karfi irinsu Rasha da Burtaniya da Faransa harta Isra’ila da Iran da Saudiya za su shigo.

Yana mai cewa, “kafa irin wannan hedikwatar na buÉ—e Æ™ofa ga Æ™ulla sauye-sauye a gwamnati da tilastawa gwamnatocin Afirka kan wasu ra’ayoyi kuma fitar su akwai wahala”.

“Abin kunya ne a ce har yanzu Æ™asashen Afirka na gayyatar turawa duk da shekarun da aka kwashe na daÆ™ile mulkin mallaka.”

Shehu Sanu ya ce muddin irin waÉ—annan rundunoni suka shigo Najeriya fitarsu za ta yi wahala, domin maganar ta wuce ta tsaro, za ta haifar da gasa ne tsakaninsu.

A cewar Sanata Sani dawowar ƙasashen yamma nahiyar Afirka ba zai kawo karshen matsalolin da ake fuskanta game da tsaro ba, yana mai cewa hadin-kai ake bukata da kafa rundunar tsaro ta Afirka domin yakar matsalolin tsaron nahiyar.

Sai dai Sanatan ya ce akwai bukatar neman taimakon kuɗaɗe da kayan yaƙi wajen cimma waɗannan burukan.

Sharhi

Matsalar tsaro dai a ƙasashen Afirka na sake tabarbarewa musamman a yankunan Sahel da tsakiyar Afirka.

A Najeriya lumura ba su sauya ba, haka zalika a kullum labarin tsaron ake musamman a makonnin baya-bayan nan da hare-hare suka yawaita.

Ƙungiyiyon kare hakkin bil adama irinsu na cewa gwamnatin Najeriya ta nuna abin da kawai za a iya kira tsagwaron rashin iya mulki, kuma ta gaza sauke nauyinta na kare rayukan al’ummarta da kawo Æ™arshen taÉ“arÉ“arewar tsaro da ke Æ™aruwa.

Ta ce rashin kataɓus ɗin hukumomi ya sa aikata laifuka da gadara na ci gaba da haɓaka kuma kashe-kashe na bazuwa a sassa da dama na ƙasar.

A cewarta lamarin ya ta’azzara raÉ—aÉ—i a zukatan al’ummomin da, da ma ke rayuwa cikin fargaba ta hari.

Gwamnatin Buhari dai a koda yaushe na iÆ™irarin cewa tana yakar Æ´an bindiga da ke sukurkuta lamuran tsaro, sai dai masana na sake jadada cewa babu kayan yaki a hannun jami’an tsaro da ya kamata su kare kasar da dukiyoyi.

More News

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Wani mutumi ya kashe mahaifiyarsa a kan kudi

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Osun sun kama wani mazaunin kauyen Kajola da ke kusa da Apomu a jihar mai suna Lukman Adejoju bisa...

Mayaƙan Boko Haram Biyu Sun Miƙa Kansu Ga Sojoji

Rundunar dakarun soja ta ƙasa da ƙasa wato Multi National Task Force(MNJTF) a turance shiya ta 3 dake Monguno a Najeriya ta bayar da...

Sojoji a birnin Ibadan  sun kama Æ´an fafutukar kafa Æ™asar Oduduwa

Dakarun rundunar sojan Najeriya  sun samu nasarar kama wasu mutane masu fafutukar kafa ƙasar Oduduwa a birnin Ibadan na jihar Oyo. Masu fafutukar sanye da...