Afirka ta Kudu: Shugaban da ke yaki da cin hanci ya shiga tsaka-mai-wuya

0
Cyrill Ramaphosa
Image caption

Mista Ramaphosa ya maye gurbin Shugaba Jacob Zuma da ya yi murabus a watan Fabrairun bara

Shugaban Afirka ta Kudu ya yi watsi da zargin da ake yi masa na cewa ya yi karya ga majalisar dokokin kasar, inda ya ce zai je kotu domin ya wanke kansa.

Cyril Ramaphosa na mayar da martani ne kan wani rahoton da ofishin babban mai yaki da cin hanci da rashawa na kasar ya fitar.

Shugaba Ramaphosa ya ta kumfar baki kan zargin cewa ya tafka karya ga majalisar dokokin kasar a bara.

A lokacin, ya musanta bayanan da ke cewa ya karbi tallafin yakin neman zabe daga wani kamfani da ake ce-ce-ku-ce a kansa, amma daga baya sai ya ce an bashi bayanan ne a jirki ce.

Masu adawa da shi sun ne mi da ya yi murabus har sai an kammala bincike kan lamarin.

Sai dai Mr Ramaphosa ya shaida wa wani taron manema labarai a ranar Lahadi cewa, zai ci gaba da mulkinsa, sannan ya yi watsi da munanan zarge-zargen da babban mai gabatar da karar ya yi masa da cewa cike suke da kuskure, kuma sun sabawa doka.

Wannan dai ba shi ne karon farko da za a mika wani lamari da jama’a da yawa ke wa kallon na siyasa ba ne ga kotunan kasar wadanda ayyuka suka yi musu yawa.

Magoya bayan shugaban sun zargi mai gabatar da karar da sanya siyasa a lamarin – ta hanyar yin aiki tare da masu adawa da Mr Ramaphosa a jam’iyyar ANC mai mulkin kasar.

Sai dai shugaban bai fito fili ya bayyana hakan ba a jawabin da ya yi, amma ya amince cewa akwai sabani a jam’iyyar, sannan ya rinka nanata bukatar a yaki cin hanci da rashawa a dukkan hukumomin gwamnati.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here