Afghanistan: Wanne kayan agaji kasar take bukata yayin da hunturu yake shigowa?—BBC Hausa

  • Daga Shruti Menon
  • BBC Reality Check
Kayan agaji a Afghanistan

Asalin hoton, Getty Images

Kungiyoyin agaji a Birtaniya suna ci gaba da nuna damuwa kan tsananin bukatar taimakon da ‘yan Afghanistan ke yi, daidai lokacin da ‘yan kasar miliyan takwas ke fuskantar barazanar fadawa matsananciyar yunwa sakamakon matsanancin sanyin da ake yi.

Yawancin kasashe sun dakatar da kai agaji Afghanistan tun bayan da kungiyar Taliban ta karbe gwamnati a watan Agusta.

Kungiyoyin agaji sun fara gangamin kira ga al’umma su kawo wa kasar agaji, domin magance matsalar. Mun yi nazari kan abin da ya kamata a yi da wadanda za su bayar da agajin.

Su wane ne suke bayar da agaji?

Kawo yanzu a wannan shekarar an samu dala biliyan 1 da miliyan 600 kadai aka samu na tallafi ga Afghanistan, kamar yadda ofishin agaji na Majalisar Dinkin Duniya wanda ke aikin agaji a Afghanistan ya bayyana.

A ko da yaushe Amurka ce a sahun gaba na bayar da agaji, sai kuma Tarayyar Turai, duk da cewa wasu daga cikin kasashe kamar Jamus na kara kudaden.

Gabanin Taliban ta karbe kasar a watan Agusta, kusan kashi 80 cikin 100 na kasafin kudin tsohuwar gwamnatin Afghanistan na zuwa ne daga kudaden agajin da kasashen waje ke bayarwa.

Duk da cewa an dakatar da yawancin tallafin da ake bai wa gwamnati, amma kungiyoyin agaji na ci gaba da taimaka wa ‘yan kasar.

A watan Oktoba, kungiyar Tarayyar Turai ta yi shelar neman dala biliyan daya na agaji, kuma kasashe da dama makofta irin Pakistan da Indiya na kai agajin abinci da magunguna kai-tsaye ta hanyar kungiyoyin agaji.

Masu bayar da tallafi na kasashen waje sun amince su tura dala miliyan 280 daga asusun kudaden Afghanistan da aka daskarar, domin sayen abinci da inganta fannin lafiya a kasar, kuma Bankin Duniya ya tabbatar da hakan.

Duk da ci gaba da bayar da agajin, ana ci gaba da fuskantar kalubale, kamar yadda UNOCHA, wadda ta yi kiyasin ana bukatar dala biliyan 4 da miliyan 500 domin gudanar da aikin agajin a shekara mai zuwa.

”Yanayin agajin da ake bayarwa ba zai wadatar da wawagegen gibin da ake da shi, na janyewar masu tallafi ba,” in ji Vicki Aken na kungiyar agaji ta International Rescue Committee a Afghanistan.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Kungiyar agaji ta Red Cross na ba da agajin kayan

Me ake bukatar a kara yi?

Shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadin cewa halin da ake ciki a Afghanistan ka iya zama mafi muni a duniya.

Sama da rabin ‘yan kasar da ya kai miliyan 23 ne ke fuskantar rashin abinci da tsananin bukatar shi sakamakon lokacin hunturun da aka fara shiga a watannin nan.

“Bukatar na da girman gaske. Zai yi matukar wuya a bayyana ainahin abin da ake bukata,” in ji Mis Aken ta IRC.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Yawancin ‘yan Afghanistan sun dogara ne da abincin agajin da ake kai wa

UNOCHA ta ce tsakanin watan Satumba zuwa Nuwambar shekarar nan, kusan mutum miliyan takwas aka bai wa tallafin abinci.

Sannan sama da mutum 200,000 da ke fama da rashin ruwa sakamakon fari an kai musu tankokin ruwa.

Irin wannan lokacin a shekarar da ta gabata, sama da yara 200,000 aka yi wa magani sakamakon rashin abinci mai gina jiki, kuma miliyoyin yaran ne suka samu tallafin magani, da sauran agajin da Hukumar Lafiyar ta Duniya ta aike.

Ofishin ‘yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya shi ma ya bayar da irin nashi tallafin na kayayyaki, ciki har da na’urar dumama daki da aka sanya a tantunan ‘yan gudun hijirar domin shan dumi a watannin hunturu.

Amma duk da hakan kungiyoyin agajin na sake kiran a karo tallafi, sakamakon halin da kasar ke ciki na kara munana.

“Duk abin da za mu samar, tamkar digon ruwa ne a cikin teku,” in ji Ingy Sedky na kungiyar Red Cross.

Red Cross ta ce kashi 60 na asibitocin da suka duba, ba su da shirin samar da abinci mai gina jiki ga yara kamar yadda Afghanistan ke bukata.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Shirin samar sa abinci na MDD na ba da agaji a yankin Kandahar

Ta yaya agajin ke isa Afghanistan?

An ci gaba da kayan yawancin agajin ta mota – ana amfani da iyakar Afghanistan da Pakistan, da Iran, da Turkmenistan, da Uzbekistan, da Tajikistan da kuma Kazakhstan.

Duk da tsauraran matakan da aka dauka na kai-komon mutane a iyakokin kasashen, UNOCHA ta ce a bude suke ga kungiyoyin agajin da suke kai kayan taimako.

Yawancin jiragen fasinja sun dakatar da sufuri daga Kabul, amma kungiyoyin agaji da gwamnati na amfani da jirage domin kai agajin gaggawa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Iran na kai agaji Afghanistan ta kasa da ta sama

Shirin samar da abincin ya ce su na iya kai agaji ta kasa da sama zuwa yankunan kasar.

Har wa yau, babban kalubalen da suke fuskanta shi ne rarrabawa kayan cikin Afghanistan musamman yankuna ma su sarkakiya da barazanar tsaro.

Red Cross a Afghanistan ta ce halin na nan yadda ya ke cike da tashin hankali, da wuya a fayyace maka girman matsalar ko bayyana yadda ake ciki saboda ko wanne lokaci fada ko tarzoma za ta iya barkewa.

Haka kuma, IRC ta na bai wa mutane tallafin kudade, saboda durkushewar bankin Afghanistan a watan Agusta ya sanya samun kudi a bankuna abin tashin hankali ne.

Yayin da aka fara muku-mukun sanyi, kungiyoyin agaji sun mayar da hankali wajen bai wa ‘yan kasar tallafin abinci da matsuguni a yankunan da dusar kankara ke gab da fara zuba, inda samun hanyar mota zai yi matukar wuya, ya yin da jiragen sama ba ma sa samun damar sauka baki daya.

(BBC Hausa)

More from this stream

Recomended