WASHINGTON D.C. —
Hukumar da ke yaki da yaduwar cututtuka ta NCDC a Najeriya ta ce adadin mutanen da suka mutu sanadiyyar cutar coronavirus a kasar ya kai 590.
Hukumar ta bayyana hakan ne a shafinta na Twitter a daren jiya Talata.
Alkaluman da hukumar ta NCDC ta fitar a ranar Litinin ya nuna mutum 573 ne suka mutu.
Hakan na nufin an samu karin mutum 17 kenan a yinin ranar Talata.
Izuwa yanzu jimullar mutanen da suka kamu da cutar a duk fadin kasar ya kai 25,694 inda Lagos ta kasance jihar da ta fi galabaita a yawan masu cutar.
Hukumar ta ce cikin wannan adadi an sallami mutum 9,746.