Hukumomin Libya sun ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa da guguwa a kasar ya zarce 6,000.
Sabbin alkaluman da gwamnatin Libiya ta fitar a ranar Larabar sun kara da cewa har yanzu dubban mutane ne suka bace sakamakon wannan mummunan lamari.
A cewar hukumar Majalisar Dinkin Duniya sama da mutane 30,000 ne suka rasa matsuguni sakamakon ambaliyar ruwa.
Wannan na zuwa ne bayan wata mummunar girgizar kasa ta afku a ƙasar Morocco inda sama da mutum 2,000 suka rasa rayukansu, tare da hasarar dukiya.