Abin lura kan coronavirus a Kano – AREWA News

Cikin kwanaki hudu har an samu mutum guda ya mutu da cutar Coronavirus a Kano, wannan kan iya nuna cewa tuni mutane suna dauke da wannan cuta a wannan jiha, Amma suka yi likimo.

Saboda gudun irin haka a ke ta kira cewa a yi maza a kulle Kano, saboda kowa ya zauna wuri daya. Har sai cutar ta taso an gano wanda ke dauke da ita da wanda ba shi da ita.

Abunda Zai baka mamaki shine har yanzu Kuma har gobe mutane na fita daga Kano Kuma suna dawowa Kano, ta dukkan mashigar ta, saboda Sam ba su ma dauki abunda gomnatin Kano ke fadi da muhimmanci ba, ita kan ta gomnatin ta kasa Mai da hanakali wajen rufe iyakokin ta da hana mutane shigowa, wannan shine babban kalubale da kan iya addabar wannan gari.

Kano dai kam ta harbu, Yanzu abunda yayi saura shine ya zama dole a rufe dukkan jihohin Arewa kargam, a hana dukkan wani shiga ta kowacce hanya, domin idan wannan cuta ta fita daga Kano babu makawa tana iya shiga ko ina, kamar yadda ta fita daga Lagos zuwa sauran jihohin kudanci.

More from this stream

Recomended