‘Abin da ya sa ba mu yi wa ‘yan China gwajin coronavirus ba’

.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Gwamnatin Fiilato ta ce bata yi wa ‘yan Chinar nan uku da aka killace gwajin cutar coronavirus ba domin gano ko suna dauke da cutar ko kuma ba su da ita.

Kwamishinan lafiya na jihar Dakta Nimkong Ndam ne ya shaida wa BBC hakan inda ya ce ko da jami’ansu suka je wurin ‘yan Chinar da aka killace, sun yi musu tambayoyi ne kawai da kuma duba takardunsu.

Ya bayyana cewa sun gano cewa an yi wa ‘yan Chinar gwaji a Addis Ababa, haka kuma da suka sauka a Abuja ma an yi musu gwaji, wannan dalili ne ya sa suka gamsu da cewa babu wasu alamun cutar tattare da su.

Ya ce ”Mun duba cewa an yi musu gwaji, sun zo a kan ka’ida, suna da takardun tafiya”.

Sai dai ya bayyana cewa za su ci gaba da zama killace sai zuwa 11 ga watan Maris kafin su fara walwala cikin jama’a kamar kowa.

Mista Ndam ya kuma kara bayar da shawara kan duk wanda ya yi tafiya zuwa wata kasa da aka samu bullar cutar coronavirus, mutum ya killace kansa da kansa zuwa a kalla mako biyu kafin ya fara shiga cikin mutane.

A ranar Asabar ne dai ma’aikatar lafiya a jihar Filato da ke arewa maso tsakiyar Najeriya ta tabbatar da killace wasu ‘yan kasar China uku saboda fargabar coronavirus.

Lamarin ya faru ne bayan wasu ‘yan kasar Chinar uku da ke aiki a wani wurin hakar ma’adanai a garin Wase sun dawo daga tafiya.

Wannan ne ya sa da isarsu kamfanin, sai ‘yan uwansu ‘yan China wadanda ba su yi tafiya ba suka hana su shiga kamfanin sakamakon tsoron da suke yi ko kuma fargabar kada a ce sun dauko musu cutar coronavirus sun kawo musu.

Wannan dalilin ne ya sa ma’aikatar lafiya tare da hadin gwiwar hukumar da ke kula da shige da fice da kuma ‘yan sanda suka tura tawaga zuwa garin Wase domin likitoci su yi musu gwajin cutar ta coronavirus.

More News

Ƴan sanda sun kama masu sayen kuri’a a zaben gwamnan Edo

Jami'an rundunar ƴan sandan Najeriya sun kama wasu mutane 9 da ake zarginsu da sayen kuri'a da kuma mallakar kuri'ar da aka riga aka...

Ƴansanda sun kama muggan ƴan fashi da makami

Jami’an hukumar ‘yan sanda reshen Elemoro reshen jihar Legas sun kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a fashi da makami a...

An kama wasu mutane biyu da hodar ibilis a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta sanar da kama wasu mutane biyu da aka samu ɗauke da ƙunshin hodar ibilis mai yawan gaske. Mai magana...

Ƴan sanda sun kama wani mutum ɗauke da bindigogi 20 a Kaduna

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce jami'anta sun kama wani  riƙaƙƙen mai safarar bindiga inda aka same shi da bindigogin AK-47 ƙirar gida...