Abdul Aziz Yari ya dauki nauyin karatun dalibai 1,700 a Jihar Zamfara

Tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma sanata mai wakiltar mazabar Zamfara ta yamma, Abdulaziz Yari Abubakar, ya baiwa ‘yan asalin jihar 1,700 tallafin karatu a jami’o’in Najeriya daban-daban.

Shugaban kwamitin shirin bayar da tallafin karatu na A.A Yari, Sanata Tijjani Yahaya Kaura, ya shaida wa manema labarai a wani taron manema labarai cewa, an kaddamar da shirin ne a kokarinsa na daukaka darajar ilimi a jihar.

Ya ce a karkashin shirin, za a tantance wadanda suka cancanta daga gidaje marasa galihu wadanda iyayensu ba za su iya daukar nauyin ‘ya’yansu zuwa manyan makarantu ba.

Kaura ya ce za a ba wa duk wadanda suka ci gajiyar tallafin karatu a fadin jihar ba tare da la’akari da bambancin addini ko jam’iyyar siyasa ba.

A cewarsa, kwamitin shirin bayar da tallafin karatu na A.A Yari ya kammala shirin fara rabon fom ga wadanda suka ci gajiyar shirin a karkashin kwamitin gudanarwa na kowace kananan hukumomi 14 na jihar.

More News

Ƴan ta’adda sama da 260 sun miƙa wuya ga jami’an tsaro

Yayin da dakarun Operation Lake Sanity 2 ke kara kai hare-hare, rundunar hadin gwiwa ta Multinational Joint Task Force (MNJTF) ta yi nasarar karɓar...

Ƴan majalisar wakilai sun rage albashinsu da kaso 50

Mambobin majalisar wakilai ta tarayya sun amince su rage albashinsu da kaso 50  na tsawon watanni 6 a matsayin nasu sadaukarwar da kuma nuna...

Tinubu ya amince da mafi karancin albashi na N70,000

Shugaba Bola Tinubu ya amince da N70,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikatan Najeriya, inda ya yi alkawarin sake duba dokar mafi karancin...

An kama ɗan sanda kan zargin aikata fashi da makami

Wani jami'in ɗan sanda mai suna Aminu Muhammad dake aiki da rundunar ƴan sandan jihar Kogi ya faɗa komar abokan aikinsa ƴan sanda kan...