Abdul Aziz Yari ya dauki nauyin karatun dalibai 1,700 a Jihar Zamfara

Tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma sanata mai wakiltar mazabar Zamfara ta yamma, Abdulaziz Yari Abubakar, ya baiwa ‘yan asalin jihar 1,700 tallafin karatu a jami’o’in Najeriya daban-daban.

Shugaban kwamitin shirin bayar da tallafin karatu na A.A Yari, Sanata Tijjani Yahaya Kaura, ya shaida wa manema labarai a wani taron manema labarai cewa, an kaddamar da shirin ne a kokarinsa na daukaka darajar ilimi a jihar.

Ya ce a karkashin shirin, za a tantance wadanda suka cancanta daga gidaje marasa galihu wadanda iyayensu ba za su iya daukar nauyin ‘ya’yansu zuwa manyan makarantu ba.

Kaura ya ce za a ba wa duk wadanda suka ci gajiyar tallafin karatu a fadin jihar ba tare da la’akari da bambancin addini ko jam’iyyar siyasa ba.

A cewarsa, kwamitin shirin bayar da tallafin karatu na A.A Yari ya kammala shirin fara rabon fom ga wadanda suka ci gajiyar shirin a karkashin kwamitin gudanarwa na kowace kananan hukumomi 14 na jihar.

More News

Sojoji sun kama Æ´an bindiga biyu da suka je asibiti a duba lafiyar su

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun samu nasarar kama wasu Æ´an bindiga biyu dai-dai lokacin da suka je asibiti domin a duba lafiyar su a...

Sojoji sun kama Æ´an bindiga biyu da suka je asibiti a duba lafiyar su

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun samu nasarar kama wasu Æ´an bindiga biyu dai-dai lokacin da suka je asibiti domin a duba lafiyar su a...

Gwamnatin tarayya ta sanar da ranar hutun bikin samun Æ´ancin kai

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Talata, 1 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutun bikin tunawa da ranar da Najeriya ta samu Æ´an cin...

Jami’an EFCC sun kai samame gidajen kwanan É—aliban UDUS

Jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) sun kai wani samame da tsakar dare a kan gidajen kwanan dalibai na...